14 Afirilu 2020 - 05:53
Kasashen OPEC Sun Cimma Matsaya Kan Rage Yawan Man Fetur

Kasashe masu arzikin man fetur mambobin kungiyar OPEC, sun cimma daidaito a tsakaninsu, ta rage yawan man fetur da suke samarwa a wani mataki na shawo kan matsalar faduwar farashin man.

(ABNA24.com) Kasashe masu arzikin man fetur mambobin kungiyar OPEC, sun cimma daidaito a tsakaninsu, ta rage yawan man fetur da suke samarwa a wani mataki na shawo kan matsalar faduwar farashin man.

Farashin man fetur dai ya yi faduwar da ba’a taba ganin irinta ba a tsawon shekaru sakamakon matsalar annobar coronavirus da kuma sabakin dake tsakanin kasashen Saudiyya da Rasha.

Saidai a jiya Lahadi, bayan shafe tsawon kwanaki na tattaunawa ta kafar bidiyo bangarorin sun sanar da cimma daidaito kan fitar da mai ganga miliyan 9,7 a ko wacce rana daga farkon watan Mayu zuwa Yuni.


Babban sakataren kungiyar Mohammed Barkindo, ya yi maraba da matakin, wanda a cewarsa shi ne mafi mahimmanci da ba’a taba samunsa ba tsakanin mambobin kungiyar ta OPEC.

Tuni dai matakin kasashen ya sanya farashin dayen man ya dan farfado da kashi 3% a kasuwanin yankin asiya da Amurka.


/129